Amurka Tace A Shirye Take Ta Shiga Yaki Da China

Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta

Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta tabbatar da cewa zata tunkari kasar Amurka da dukkan karfinta kan ko ta ina ta fito mana a adawar da take nunawa kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hegseth yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake hira da shirin labarai na tashar talabijin ta Foxnews na Amurka.

Seketarin tsaron tsaron ya kara da cewa dok wanda yake son zaman lafiya to ya shiryawa yaki. Don haka kasar Amurka, inji Hegseth dole ta tabbatar da tana da sojojin masu karfi da makamai masu inganci don shiriwa ko ta kwana, saboda irin yadda kasar China take samun ci gaba mai yawa a bangaren tsaron kasarta.

Yace kasar China tana son ta maye gurbin Amurka a wurare da dama a duniya. Wanda hakan barazana ce gareta.

Yace ‘muna bukatar kashe kudade wa harkokin tsaro, wadanda suka hada makamai na zamani, don ganin yankin Ido-pecific ya ci gaba da zama karkashin ikon sojojin Amurka..

Jawaban da Hegseth na zuwa ne bayan da kasar china ta bayyana anniyarta na fuskantar dukkan barazanar da Amurka zata yiwa kasar, ta kara kudin fito da kasuwanci da sauransu, duk ta inda ta fito a shirye muke mu fuskanceta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments