Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10

Gwamnatin Amurka ta sanar da soke bada mafaka ga wasu kasashen duniya 19 wadanda suka hada da na Afrika guda 10. Wannan matakin, ya zo

Gwamnatin Amurka ta sanar da soke bada mafaka ga wasu kasashen duniya 19 wadanda suka hada da na Afrika guda 10.

Wannan matakin, ya zo ne bayan harin da aka kai a Washington kwanan nan, kuma ya shafi  kasashe 19, da suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, a cewar wata sanarwa da Hukumar Kula da ‘Yan Kasa da Shige da Fice ta Amurka (USCIS) ta fitar.

Sauran kasashen su ne Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela.

Sanarwar ta umarci ma’aikatan hukumar da su “rike duk fom din bukatar Zaman Mafaka, ba tare da la’akari da kasar da bakon yake ba, har sai an sake duba shi.”

Matakin ya shafi ‘yan kasashe 19 da suka shiga Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2021 ko bayan haka don tantance duk barazanar da ke akwai ga tsaron kasar da tsarin jama’a.”

Wannan shawarar ta zo ne bayan da Shugaba Donald Trump da Sakataren Tsaron Cikin Gida Kristi Noem suka yi kira da a tsaurara matakan tsaro kan shige da fice bayan harbin da aka yi wa wasu jami’an tsaron National Guard guda biyu a makon da ya gabata a Washington, D.C.

Wanda ake zargin, dan kasar Afghanistan ne mai shekaru 29 wanda aka ba shi mafaka a watan Afrilu, ya shiga Amurka a shekarar 2021 bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan kuma ya taba yin aiki a wasu hukumomin gwamnatin Amurka, ciki har da CIA, a cewar kafofin watsa labarai na Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments