Amurka ta sake hana kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kiran tsagaita bude wuta da kuma kai agajin jin kai a Gaza.
Wannan hawa kujerar na-ki shi ne irinsa na farko na sabuwar gwamnatin Trump kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan ci gaba da yakin da takeyi a gaza dama hana shigar da kayan agaji.
Daftarin kudurin da aka gabatar wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba ya bukaci “a gaggauta tsagaita wuta na dindindin” da kuma sakin wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba.
Kudirin da kasashe 10 wadanda ba mambobin kwamitin na dindindin ba suka gabatar, ya samu sahalewa daga kasashe 14, yayin da Amurka ta yi fatali da shi.
Kafin kada kuri’ar, Amurka ta ce “kudirin zai wargaza kokarin diflomasiyya na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta gaskiya, kuma zai karfafa wa Hamas,” ne in ji jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Dorothy Shea.
Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya bukaci MDD da ta dauki mataki.
Wannan matakin na ranar Laraba ya kasance karo na shida da Amurka ke toshe kudurin tsagaita wuta a Gaza tun watan Oktoban shekarar 2023.