Rahotanni daga Syria suna nuni da cewa Amurkan tana kara yawan sojojin da take da su a gundumar Hasakah dake yankin Arewa masu gabashin Syria.
Kafafen watsa labarun Syria sun ce an ga ga ayarin motocin soja 20 da su a fito daga sansanin Amurka na Ain al-Asad na Iraki, suna shiga cikin kasar inda su ka nufi gunumar Hasakah.
Jiragen sama na yaki ne suke yi wa ayarin motocin yakin rakiya,yayin da wasu sojojin musamman suke binsu a baya.
Kwanaki kadan da su ka gabata an ga wasu ayarin motocin na Amurka su 60 suna shiga cikin kasar ta Syria zuwa Dei-Zur, inda dama suke da wasu sansanoni a cikin wuraren hakar man fetur da kuma Iskar Gas mallakin Syria.