Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya.
Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da kuma wani mutum guda da ke Iran, saboda abin da sashen ya bayyana a matsayin goyon bayan shirin nukiliyar Iran.
Baitul malin na Amurka ya ce bangarorin da aka laftawa takunkumin na baya baya nan sun hada da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) da ta karkashinta, Kamfanin Fasaha na Centrifuge na Iran.
Sakataren baitul malin kasar Scott Bessent ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rikicin rikon sakainar kashi da Iran ke yi na kera makaman kare dangi ya kasance babbar barazana ga Amurka da kuma barazana ga zaman lafiyar yankin da kuma tsaron duniya.
Binciken da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya ta yi a cibiyoyin Nukiliyar Iran ya musanta ikirarin Iran na neman makaman Nukiliya.