Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya makamai mai tsoka ta Dala biliyan 142 da Saudiyya.
Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, ke gudanar da ziyara a kasar Saudiyya irinta ta farko a ketare tun bayan sake hawansa karagar mulki.
Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mafi girma a tarihi.
” Wannan yarjejeniya, wacce wani bangare ne na babban kunshin alkawurran saka hannun jari – da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 600, a cewar gwamnatin Amurka – za ta ba wa masarautar Saudiyya damar sayen “kayan aikin soja daga kamfanonin tsaron Amurka goma sha biyu,” musamman a fannin tsaron sararrin samaniya, makamai masu linzami, tsaron teku da tsarin sadarwa.
A wani labarin kuma shugaban kasar ta Amurka ya sanar da dage takunkumi kan kasar Siriya.
“Zan ba da umarnin dage takunkumin da aka kakaba wa Siriya domin ba su dama ta daukaka,” in ji shugaban na Amurka, wanda ke nuni da cewa ya cimma wannan matsaya ne bayan bukatar gaggawar da yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya yi masa.
Ana san kuma zai gana da shugaban rikon kwarya na Siriya Ahmed al-Charaa nan gaba a Saudiyyar.