Amurka Ta Kashe Dala Biliyan 48 A Yaki Da Iran

Wannan ya nuna karuwar kusan kashi 26 cikin 100 idan aka kwatanta da kiyasin da Ofishin ya yi a baya.

Wani jami’in Pentagon ya ce Amurka ta kashe sama da dala biliyan 48 tun soma yaki da Iran a watan Fabrairu.

“Ya zuwa ranar 13 ga Nuwamba, Amurka ta kashe dala biliyan 48.3,” in ji Arthur Miller, mataimakin babban jami’in Pentagon, ga ‘yan Majalisar Dokoki.

Wannan ya nuna karuwar kusan kashi 26 cikin 100 idan aka kwatanta da kiyasin da Ofishin Kasafin Kudi na Majalisa (CBO) ya yi a baya, wanda ya kiyasta kudin yakin ya kai dala biliyan 38 a ranar 1 ga Agusta.

“Wannan ya hada da harsasai, kayan aiki, da kudaden aiki,” in ji Miller a a gaban ‘yan majalisa.

Wannan adadi bai kunshi sansanonin Amurka da aka lalata a Gabas ta Tsakiya, wadanda wasu daga cikinsu suka fuskanci mummunan hari daga jiragen sama marasa matuki na Iran da kuma hare-haren makamai masu linzami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted