Amurka ta karbi Amurkawa 3 da suka yi yukurin juyin mulki a Congo

Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna

Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna hannun Amurka bayan yanke hukuncin da aka yi a kansu a makon jiya, kamar yadda wasu jami’an Amurka da na  fadar shugaban kasar Kongo suka bayyana ga kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan  Talata.

A ranar 19 ga Mayu, 2024, wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji sun mamaye ofishin shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi bayan da suka mamaye gidan ministan tattalin arzikin kasar mai barin gado kuma dan takarar shugaban majalisar dokokin kasar Vital Kamerhe.

An bayar da rahoton mutuwar mutane shida da suka hada da jami’an ‘yan sanda biyu a lokacin yunkurin juyin mulkin.

An kammala yanke shawarar mika Amurkawan ne yayin da babban mai baiwa shugaba Donald Trump shawara kan harkokin Afirka, Massad Boulos, ya gana da shugaba Felix Tshisekedi a Kinshasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments