Amurka Ta Kara Kakabawa Kungiyar Ansarullah Ta Yemen Takunkuman Tattalin Arziki

Gwamnatin shugaban Donal Trump ta kara kakabawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen takunkuman tattalin arziki wadanda suka hada da man fetur, da dangoginsa, makamai da

Gwamnatin shugaban Donal Trump ta kara kakabawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen takunkuman tattalin arziki wadanda suka hada da man fetur, da dangoginsa, makamai da kuma duk abubuwan da ake iya samar da makamai da su.

Shafin labarai na yanar Gizo ‘Arabmews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa takunkuman sun hada da mutane 21 da kuma wasu hukumomi da kuma wani jirgin ruwa. Hakama wasu kamfanoni a kasar ta Yemen, Omman da kuma Hadaddiyar daular Larabawa.

Ma’aikatar baitul-malin Amurka ta kara da cewa kungiyar Ansarallah barazana ce ga Amurka kuma tana aikata ayyukan da ta kira ta’addanci, inda take kai hare-hare kan jiragen kasuwanci  wadanda suke wucewa ta tekun red sea.

Scott Bessent sakataren kudi na Amurka ya kara da cewa wadan nan takunkuman kari ne kan wadanda ma’aikatar ta dorawa kungiyar ta Huthi ko ansarullah a baya, wadanda suka takaita hanyoyin samun kudi na kungiyar.

Babban kamfanin huthawa da takunkumin ya shafa inji Scott shi ne Janatt Al-Anhar wanda yake da rijista a kasar Hadaddiyar larabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted