Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma Sa’ada.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga doron kasa.
Tun ranar Asabar da ta gabata ce sojojin Amurka da Burtaniya wadanda suke da jiragen yakinsu a cikin tekun maliya da wasu wurare a yakin suka fara kaiwa kungiyar hare-hare saboda goyon bayan ga HKI.
Kafin haka dai kungiyar Ansarullahi ta bawa HKI kwanaki huda ta kawo karshen kofar ragon da ta yiwa falasdinawa kimani miliyon biyu a gaza, inda suka hana shigowar abinci da abin sha shiga cikin yankin.
A lokacinda wa’adin ya cika ne HKI ba ta amsa kiran kungiyar ba, sai ta dauki matakin hana jiragen ruwan HKI da wadanda suke zuwa can wucewa ta tekun maliya.
Amurka ta shiga yakin ne da sunan hana kungiyar Ansarallah hana zirga-zirgan jiragen ruwan kasuwanci a tekun maliya.