Amurka ta kai sabbin munanan hare-hare ta sama har sau 22 a wasu larduna da dama na kasar Yemen, jim kadan bayan kai wa kasar hare-hare da dama makamancin haka.
A cewar majiyoyin na Yemen, wadannan sabbin hare-hare na Amurka sun auna yankuna daban-daban a ranar Laraba, ciki har da babban birnin kasar Sanaa da lardin Ibb da ke tsakiyar kasar.
A Sana’a, an kai hare-hare ta sama guda takwas. Har yanzu ba a tabbatar da asarar rayuka ba, amma hare-haren sun shafi muhimman ababen more rayuwa, lamarin da ke kara tabarbare yanayin rayuwa ga fararen hula.
An sami adadin wadanda suka mutu mafi muni a lardin al-Hudaydah da ke yammacin kasar, inda aka tabbatar da mutuwar fararen hula 6 da suka hada da yara biyu da mace daya.
Akalla wasu mutane 16 sun jikkata, wadanda da dama daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Da wadannan hare-hare, jimillar hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen ya kai 50 cikin sa’o’i 24 kacal.