Amurka Ta Kai Hare-hare Akan Birane Mabanbanta Na Kasar Yemen

Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen. Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya

Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda  yake gabashin birnin San’aa.

Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka din sun kai hare-haren ne a tsakanin marecen jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis.

Daga cikin wuraren da aka kai wa harin jiya da marecen da akwai Sahlin dake karamar hukumar Ali-Salim. Sau 6 Amurkan ta kai wa yankin hare-hare.

Da safiyar yau Alhamis kuwa jiragen yakin na Amurka sun kai hare-hare a gundumar Sa’adah.

Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren su ne, al-tahita, dake kudancin gundumar Haudaidah, a yammacin kasar ta Yemen.

Amurka tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda  bayar da kariya ga HKI, da zummar hana Yemen kai hare-hare akan manufofin ‘yan sahayoniya a ruwan tekun ” Red Sea”.

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ba za ta taba daina kai wa HKI hare-haren ba har sai idan an daina kai wa Gaza hari. Bugu da kari ta sanar da cewa;za ta ci gaba da hana jiragen ruwa wucewa ta tekun “Red Sea” har zuwa lokacin da za a kawo karshen hana shigar da kayan agaji cikin yankin na Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments