Rahotanni daga kasar Yemen sun ambaci cewa jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-hare a yankuna mabanbanta na kasar Yemen da su ka hada da birnin San’aa.
Tashar talabijin din al-masirah ta ambaci cewa; jiragen yakin Amurka sun kai hare-haran ne har sau 7, biyu a cikin yankin Hamadan, da Banu Hashish sai kuma babban birnin kasar Sanaa.
Kawo ya zuwa babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko shahada sanadiyyar wannan harin.
Amurkan dai tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda taimakawa HKI a yaki, da kokarin hana dakarun Ansarullah ci gaba da kai hare-hare akan manufofin HKI.
A daren jiya Alhamsi shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; hare-haren da Amurka take kai musu ba su yi wa makaman da suke da su illa ba,kuma akasin haka suna kara musu azama ne.
Sojojin Yemen suna kai hare-hare a HKI saboda yin matsin lamba akan HKI ta dakatar da hare-haren da take kai wa Gaza, sannan kuma da mayar da martani akan jiragen dakon jiragen yaki na Amurka a tekun “Red Sea’ bayan da su ka fara kai wa Yemen din hari.