Amurka Ta Hau Kujerar Na-ki Kan Bukatar Gaggauta Tsaigaita Wuta A Gaza

Amurka ta hau kujerar na-ki a kan bukatar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gabatar don dakatar da bude wuta nan take kuma

Amurka ta hau kujerar na-ki a kan bukatar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gabatar don dakatar da bude wuta nan take kuma ba tare da wani sharadi ba a yakin Gaza.

Shirin ya kuma jaddada bukatar sakin dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da bai wa fararen hula a Gaza damar samun ruwa da abin da duk suke bukata na rayuwa da kuma taimako.

Dukkanin sauran mambobin kwamitin su 14 sun jefa kuri’ar amincewa da shirin, saidai ya ci karo da kin amincewar Amurka babbar kawa ga Isra’ila.

Darektan kungiyar kare hakkin dan’Adam na majalisar dinkin duniya, Louis Charbonneau, ya zargi Amurka da abin da ya kira amincewa da miyagun laifukan keta haddin dan’Adam da Isra’ila ke yi.

Daftarin, ya bukaci “tsagaita wuta cikin gaggawa, ba tare da sharadi ba kuma na dindindin wanda dole ne dukkan bangarorin su mutunta” da kuma “sakin dukkan wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba”.

Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama sun bukaci a tsagaita bude wuta Gaza domin isar da agajin gaggawa ga jama’ar Zirin, a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare hare ba dare ba rana a yankin datayi wa kawayen.

A halin da ake Adadin wadanda sukayi shahada a Gaza ya kai 43,985 a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin tun ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments