Gwamnatin kasar Amurka ta ce bata bukatar samuwar jkadan kasar Afrika ta kudu Ebrahim Rasool a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa Rasool mutum ne wanda yake nuna wariya, yake kuma kin Amurkawa. Don haka bama da abinda zamu tattauna da shi, kawai bama son ganinsa a cikin kasar babba.
Rubio bai bayyana dalilan daukar wannan matakin a kan jakadan ba, amma hakan ya faru ne bayan da Jakadan Rasool ya wata cibiyar bincike na Afrika ta kudu inda a jawabin da ya gabatar ya zargi shugaban kasar Amurka Donal Trump da, da samar da shirin “sake maida Amurka kasa babba” da wani shirin fifita fararem Amurka a kan sauran mutane a duniya.
Labarin ya kara da cewa tun lokacinda Trump ya sake dawowa fadar white house aka hana jakadan Afirka ta kudu a kasar ganawa da jami’an fadar white House kamar yadda ya dace. Fakon haka Amurka ta yi barazanar dakatar da tallafin da take bawa kasar Afrika ta kudu saboda karar da ta shigar kan HKI wacce ta aiwatar da kissan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 har zuwa yanzun. Banda haka kasar ta sami goyon baya daga kasashen duniya da dama. Kuma gwamnatin Amurka ta bukata Afirka ta kudu ta janye karar amma taki amincewa.
Ya zuwa yanzu dai kotun ta ICC ta fidda sammacin kama Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yauf Galant. Kafin haka dai Ebrahim Rasool ya taba zaman jakadan Afrika ta kudu a kasarAmurka daga shekara ta 2010-2015 a lokacin shugabancin Barak Obama