Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta har kimani 30 a kasashen duniya, amma mafi yawansu a kasashen Afirka.
Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkan na fadar cewa gwamnatin shugaban Trump tana son ta rage yawan kashe kudade a ma’aikatar don amfani da su a cikin gida.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin Amurka tana son rage kudaden da take kashewa ma’aikatar harkokin wajen kasar da kashi 50% da kuma rage tallafin da take bawa wasu kungiyoyi a wadan nan kasashe har na kashi 75%.
Labarin ya kara da cewa kasashen da shirin ya shafa dai akwai Lesotho, Eritrea, Afrika ta tsakiya, Congo Brazavile, Gambia, Sudan ta kudu,. Banda wadannan za’a rufe kananan ofisoshin jakadanci da ke birnin Durban na Afrika ta kudu, da kuma na Douala, da ke kasar Cameroon. Labarin yace ayyukan wadannan ofisoshin jakadanci zasu kuma ga kasashe makobta.
A kasahen turai da Asiya kuma Amurka zata rufe ofisoshin jakadancinta a tsibirin Malta, Luxembourg, da kuma wasu kananan ofisoshin jakadancin kasar a tarayyar Turai da Asiya.