Rahotanni na cewa Amurka na matsa wa Birtaniya lamba don kare firaministan isra’ila Benjamin Netanyahu daga sammacin kame shin a Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.
A cewar bayannan Amurka na matsa kaimi wajen ganin Birtaniya bata aiwatar da matakin da zai kai ga kama Netanyahun ba kan laifukan yaki a kan Falasdinu.
Lauyan kare hakkin bil adama Geoffrey Robertson ya yi ikirari game da matsin lambar da Amurka ke yi a wata makala da aka buga a jaridar The Guardian ranar Laraba.
A watan Mayu ne, babban mai shigar da kara na kotun ICC, Karim Khan, ya bukaci a ba da sammacin kama Netanyahu da ministan tsaron Isra’ila, Yoav Gallant, bisa zargin aikata laifukan yaki a Gaza.
Rahotanni sun ce Firaministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu yana duba yiwuwar kauce wa shiga Turai a kan hanyarsa ta zuwa Amurka saboda ya guje wa yiwuwar kama shi.
Wannan shawarar na da nasaba da fargabar cewa kasashen Turai za su iya tilasta wa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) sammacin kama Netanyahu kan yiwuwar sa hannu a laifukan yaki da kisan kiyashi a Gaza na Falasdinu.
Ana tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa, hukuncin da ta yanke na baya-bayan nan ya umurci Tel Aviv da ta gaggauta dakatar da aikin soji a kudancin birnin Rafah.
Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 38,243 akasarinsu mata da yara, ya kuma raunata wasu 88,033 sannan ana hasashen cewa aƙalla sama da mutum 10,000 ke binne a karkashin baraguzan gine-gine.