Amurka, Faransa, Jamus Da Birtaniya Sun Bukaci A Kwantar Da Hankali A Siriya

Kasashen Amurka da Faransa da Jamus da kuma Birtaniya sun yi kiran da a kwantar da hankali a kasar Siriya. A cikin wata sanarwar hadin

Kasashen Amurka da Faransa da Jamus da kuma Birtaniya sun yi kiran da a kwantar da hankali a kasar Siriya.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a ranar Lahadi kasashen sun bukaci a warware rikicin kasar Syria, inda kungiyoyin ‘yan tawaye suka karbe iko da wasu yankuna da dama.

Sanarwar ta ce ‘”Muna kira ga dukkan bangarorin da su sassauta tare da kare fararen hula da kayayyakin more rayuwa da gujewa wargajewar da zata kawo cikas ga isar da kayan agaji,”

Haka zalika a cewar sanarwar habakar rikicin ya jaddada bukatar gaggawa ta tattaunawar siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments