Amurka da Iran zasuyi tattaunawa ta hudu a ranar Lahadi

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi.

Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar.

Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu kasar Oman ta tattauna da bangaren waccen bangaren.

Babban mai shiga tsakani na Iran ya jaddada cewa tattaunawar Tehran da Washington tana ci gaba.

Iran da AMurka dai sun yi jerin tattaunawa har guda uku a Oman, sannan a Italiya sai kuma a Oman.

Dukkan bangarorin dai sun bayyana tattaunar da mai kyakyawan fata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments