The Gaza Humanitarian Foundatin (GHF) a Gaza ta bada sanarwan kawo karshen ayyukanta a Gazar makonni 6 bayan an fara abinda ake kira tsagaita wuta a Gaza.
Shafin yana gizo na labarai ‘ArabNews’ na kasar Saudiya ya nakalto shugaban hukumar John Acree yana fadar haka ya kuma kara da cewa hukumar ta cimma manufar kafata na rarraba abinci tsakanin Falasdinawa a Gaza wadanda suke mutuwa saboda yunwa bayanda HKI ta hana shigowar abinci na tsawon kwanaki kimani 90 ko watanni 3.
Gwamnatin kasar Amurka ta da HKI ne suka kafa hukumar bada agajin bayan sun kori dukkan kungiyoyin bada agaji a yankin. Sannan sun yi amfani da hukumar don kissin Falasdinawa wadanda suke takawa da kafa zuwa cibiyoyin bada abinci da suka kafa a wuraren da sai sun wuce ta gaban sojojin HKI, wadanda suke bude masu wuta.
Amma Falasdinawan basu da zabi, ko yunwa ta kashe su a cikin gaza ko kuma su je su karbi abincin da mai yuwa ba zasu dawo ba har abada.
Amurka da HKI sun kashe daruruwan Falasdinawa a cikin wannan lokacin. Acree yace sun raba kunshi abinci miliyon uku dauke da abinci miliyon 187 ga falasdinawa a lokacin da suka gudanar da ayyukansu.