Tawagar jiragen saman yaki da dama ne suka kai munanan hare-hare kan sassa daban-daban na kasar Yemen a jiya Litinin
Kafofin yada labaran kasar Yemen sun rawaito a jiya litinin cewa: Wata tawagar jiragen saman yakin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankuna daban-daban na kasar Yemen da suka hada da gundumar Bajil da wasu wurare a gundumar Al Hudaydah da ke yammacin kasar ta Yemen, da kuma gundumar Sinjan da ke birnin San’a.
Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa: Mutane 21 ne suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da aka kai kan masana’antar siminti na Bajel da ke gundumar Al Hudaydah.
A nata bangaren, tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto wani jami’in gwamnatin Isra’ila yana cewa: “Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan kasar Yemen a matsayin mayar da martani ga hare-haren makamai masu linzami da Yemen take kai wa a filin jirgin sama na Ben Gurion,” inda ya ce jiragen yakin gwamnatin Isra’ila 30 ne suka shiga cikin kai hare-hare da aka kai Yemen.
Tashar talabijin din ta kara da cewa: “Amurka ta yi ruwan bama-bamai a birnin San’a, sannan haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hare-hare kan Hodeidah,” tana mai jaddada cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Yemen na hadin gwiwa da Amurka ne, kuma Netanyahu ne ke sa ido a kai.