Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Amurka da ta kama Fira ministan “Isra’ila” Benjamin Netanyahu da yake ziyarar aiki a kasar.
A wasu jerin sakwanni da kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta duniya ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa; Yadda Amurka ta karbi bakuncin Benjamin Netanyahu alhali ana zarginsa da manyan laifuka, yana nuni da cewa ta raina kotun ta kasa da kasa.
Har ila yau kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta kuma kara da cewa; Gwamnatin da ta gabata ta Amurka a karkashin Joe Biden ta yi watsi da duk wani yunkuri na shimfida adalci a duniya, kuma shi ma shugaba Trump abinda yake yi kenan a yanzu.
Wannan ce ziyara ta farko da Fira ministan HKI Benjamin Netanyahu ya kai zuwa waje, tun bayan da kotun kasa da kasar ta fitar da sammacin kamo shi, saboda aikata manyan laifuka da su ka hada da kisan kiyashi.
A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne dai kotun kasa da kasa ta fitar da sammacin a kamo Benjamin Netanyahu da ministansa na yaki Yoav Gallant, saboda laifukan da su ka tafka a Gaza.
A karshe kungiyar kare hakkin bil’adaman ta ce, bai kamata ba a bai wa masu aikata laifukan yaki akan bil’adama mafaka.”