Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu.
Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da cewa da akwai yiyuwar a kara samun saukar mamakon ruwa sama a tsakiyar kasar, nan da wasu kwanaki masu zuwa.
Wannan ambaliyar dai wacce ta shammaci mutanen kasar, a lokacin da kungiyar agajin kasar ta sanar da cewa, tana da karancin kayan da ake da bukatuwa da su domin kai daukin gaggawa idan hakan ta faru.
Kasar Somaliya ta fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a 2023 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100, da kuma tilastawa mutane fiye da miliyan 1 yin hijira.
Sauyin yanayi yana daga cikin muhimman dalilan faruwar ambaliyar ruwa irin wannan.
Yankin zirin Afirka da gabashinta, suna cikin wuraren da sauyin yanayi yake haddasa kamfar ruwa a baya da kuma fari,da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar dabbobi masu yawa. Hakan nan kuma ya tilastawa mutanen yankin barin matsugunansu zuwa sansanonin ‘yan hijira domin samun abinda za su ci.