Alummomin duniya na ci gaba da yin Allah wadai da kisan fararen hula a Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya farke a gabar tekun Syria a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya farke a gabar tekun Syria a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa an kashe wasu iyalai baki daya a wannan tashin hankali, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin “mai matukar tayar da hankali”.

Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan kisan kiyashin da masu dauke da makamai suka aikata, tare da hukunta wadanda suka aikata laifukan.

Babban jami’in kare hakkin bil adama na MDD ya kara da cewa, “Muna samun rahotanni masu matukar tayar da hankali kan yadda ake kashe iyalai baki daya, da suka hada da mata da yara,  yana mai jaddada kira a kan dole ne a daina kashe fararen hula a yankunan gabar teku a arewa maso yammacin Syria.

Ya yi kira da a gudanar da bincike na gaskiya cikin gaggawa ba tare da nuna son kai ba, kan dukkan kashe-kashe da sauran cin zarafin da aka aikata, ya kara da cewa “wajibi ne a hukunta wadanda suka aikata hakan bisa ka’idoji da dokokin kasa da kasa.

A nasa bangaren, shugaban hukumar lafiya ta duniya ya bayyana fadan a matsayin abin damuwa sosai tare da tabbatar da cewa hakan yana yin mummunar  illa ga lafiyar mutane kai tsaye, domin kuwa a rusa cibiyoyin lafiya da motocin daukar marasa lafiya.

Tedros Adhanom ya wallafa cewa, “WHO tana aiki tukuru don isar da magunguna cikin gaggawa, don kulawa ta gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments