Al’ummar Musulmi  Tana Da Damar Sake Gina Wani Gagarumin Cigaba Na Zamani

A kasar Bangaladesh an bude taron karawa juna sani mai taken: “Samar da cigaba na musulunci ya zama wajibi domin gina al’ummar musulmi”. Taron

 A kasar  Bangaladesh an bude taron karawa juna sani mai taken: “Samar da cigaba na  musulunci ya zama wajibi domin gina al’ummar musulmi”.

Taron karawa juna sanin wanda  ofishin raya al’adu na jamhuriyar musulunci ta  Iran ta shirya a birnin Dakar, ya sami halartar masana da su ka gabatar da kasidu mabanbanta.

Shugaban ofishin raya al’adu da kuma tuntunbar juna na muulunci na Iran, Sayyid Ridha Mir Muhammadi wanda ya gabatar da jawabi, ya bayyana cewa; Wajibi ne ga al’ummar musulmi su kawar da duk wasu abubuwan dake kawo cikas wajen samun cigabansu, domin a samar da al’ummar musulmi guda daya a fadin duniya.”

Har ila yau Ridha Mir Muhammadi ya ce; A wannan  lokacin al’ummar musulmi tana da bukatuwar gina sabon cigaba da ya dace da zamanin da ake ciki,sannan ya jaddada cewa; Da akwai dukkanin abubuwan da ake bukatuwa da su domin gina wannan cigaban, illa iyaka abinda ya kamata a yi shi ne kawar da abubuwa da suke kawo cikas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments