Tahotanni sun nuna cewa alummar kasar Ecodo sun yi fatali da shawarar bada damar dawo da sansanin sojin Amurka a kasar a wani zaben raba gardama da aka gudanar a kan batun.
Dubban alummar kasar Ecodo ne suka hallar a gaban akwatunan zabe don bayyana ra’ayinsu na amincewa ko rashin amincewa da dawo da sansanin sojojin Amurka a kasar, ko a shekara ta 2008 ma sun yi watsi da kafa sansanin sojin kasashen waje saboda kare martabar kasar.
A zaben da aka gudanar ya nuna cewa kusan kaso 60 cikin dari sun ki amincewa da shirin shugaban kasar Daniel Noboa babban abokin shugaban Amurka Donald trump kuma mai goyon bayan gudanar da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya da kuma kusa da kasar venuzuwela.
Sakamakon zabe ya dakatar da Amurka na kokarin komawa sansanin sojin sama na manta dake gabar tekun pacific wanda ya kasance wajen gudanar da ayyukan sojin na washington