Mataimakin shugaban kasar Iran na Farko ya ce; Al’ummar Imam Husaini a Iran ba za su bari makiya su cimma mummunan burinsu ba
Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Muhammad Reza Aref ya rubuta a cikin wata wasika cewa: Domin kare martabar Iran da kasar al’ummar Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba barin mafarkin masu kyama ya tabbata ba.
Aref ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram a jajibirin ranar Ashura inda ya rubuta cewa: “Saboda Iran da kasar da tushen al’ummar Mabiya Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba bari mafarkin makiya ya tabbata ba.
A yammacin jiya Asabar ne Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci zaman juyayin Ashura, domin tunawa da shahadar Imam Husaini (a.s).
A daidai lokacin da ake gudanar raya daren jajibirin ranar Ashura, an gudanar da zaman makoki a Husainiyar Imam Khumaini (Allah ya tsarkake ruhinsa) tare da halartar jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khamenei da dimbin jama’a daga bangarori daban-daban na al’umma.