Alkali A Amurka Ya Umarci Gwamnatin Ta Daina Tsorata Jami’an Zabe

wani alkali a kasar Amurka ya umarci gwamnatin Trump ta daina tsoratar da jami'an zabe

Alkalin wata kotu a wata gunduma a Amurka Trina thampson ya yanke hukumci cewa gwamnatin Trump ta yi aiki wajen ikonta da tsarin mulki ya bata, kuma mai yi yuwa ta sabawa dokar hakkokin zabe ta shekara ta 1965 wadda ta haramta duk wani yunkuri na tsoratarwa ko barazana ko tilastawa ga jami’an dake kula da gudanar da zabe

Duk da cewa wadanda ake kara suna ikirarin cewa mataken da suka dauka sun yi ne da nufin dakile kada kuri’a ba bisa kaida ba daga mutane da ba yan kasa ba, amma akwai yiwuwar wadannan mataken su haifar da tsangwama ga masu gudanar da zabe, da kuma hana masu hakkin kada kuri’a damar yin hakan

Wannan hukunci ya zo ne a matsayin mayar da martani ga karar da kungiyoyin kwadago da wasu kungiyoyi daban-daban suka shigar kwana daya kafin nan, inda suka yi korafi kan gwamnatin trump saboda tsoma baki a harkokin gudanar da zaben tsakiyar wa’adi

gwamnatin trump na duba yiyuwar daukar matakin sharia akan wasu jihohi kari a lokacin da ake gabatar da zaben tsakiyar wa’adi ko kuma bayan zaben, a matsayin wani kokari na tilastawa jihohin su binciki jerin sunayen masu kada kuri’a domin gano wadanda ba yan kasa ba dake kokarin kada kuria a zaben da ake yi

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted