Aljeriya Tayi Kira Da A Dakatar Da Israila Game Da Hare-haren Da Take Kaiwa

Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai

Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan hare haren, kuma akwai dubban laifuffukan da Isra’ila ta aikata da ba’a manta ba kuma ba’a dauki wani mataki a kai ba.

Aljeriya ta yi wannan bayanin  ne bayan karuwar sukar da ake yi a kwamitin tsaro game da mataken da isra’ila ke dauka a daidai lokacin da ake cikin matsala game da isar da taimakon agaji ga alummar gaza.

A taron da kwamitin tsaro ke yi duk wata game da halin da ake ciki a yankin yammacin Asiya da suka hada da yankin falasdinu , jakadan kasar Aljeria Ammar ben Jamaa yayi tofin Allah tsine a wannan karon kan abin da isra’ila ke yi. Jamaa ya soki Isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza, abin da ya kira da wani shiri na share wata alumma a bayan kasa don hana kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai, yace ba za’a manta da dubban hujoji da ake da su kan laifukan yaki da Isra’ila ta aikata ba , don haka wadanda suka aikata laifukan ya kamata su fuskanci sharia’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments