Mai bawa jagoran Juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya sake tabbatar da cewa kasar Iran ba zata dakatar da aikin tace makamacin Uranium kamar yadda gwamnatin Amurka take so ba. Sannan ya kara da cewa kasar tana kokarin sake gabatar da wata shawara daban ga kasar Amurka.
Ali shamkhani ya fadawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon a wata hira da ta hadasu a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu suna rubutun wata shawagara ga gwamnatin Amurka dangane da hakan.
Shamkhani ya kara da cewa wasikar da Amurka aikawa Tehran bata ambaci batun daukewa kasar takunkuman tattalin arziki ko kadan ba. Ya kuma soki kasar ta Amurka a wasikar da ta aikowa Tehran ba tare da ambatun daukewa kasar takunkuman tattalin arziki ba, duk da cewa ta san hakan yana da muhimmanci ga JMI.