Jami’ar mai aikin tsarawa MDD rahoto akan Falasdinu Farencesca Albanese ta bayyana cewa; tsagaita wutar yaki da aka yi a Gaza, bai wadatar ba, wajibi ne a kawo karshen tsarin mamaya a Falasdinu.
Albanese ta kuma ce Amurka ce take bai wa ‘yan mamaya cikakken goyon baya a kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu,don haka ya zama wajibi a kawo karshen yadda ‘yan mamayar suke sarrafa albarkatun al’ummar Falasdinu,sannan kuma a tarwatsa tsarin mulkin mallaka na mamaya.
A halin da ake ciki a yanzu dai Albanese tana kasar Afirka Ta Kudu, inda take halartar taron shekara-shekara akan “Nelson Mandela” za kuma ta gabatar da jawabai a wurin.
Tun a cikin watan Mayu ne dai Amurka ta kakawa ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda matsayarta ta sukar HKI akan laifukan yaki da kuma kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Falasdinu.