Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab.
Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan.
A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata, jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National ” bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar.
A cikin watan maris da ya gabata ne shugaba Al-Sharaa na kasar Syriya ya rattaba hannu a kan wata yarjeniya da shugaban dakarun kurdawan kasar Siriya SDF Mazlum Abdi dangane da hade dakarunsa da sojojin kasar Siriya, sannan yace tsarin tarayya ya sabawa wannan yarjeniyar.