Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza

Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a

Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura.

An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin.

Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin abun tashin hankali da kuma yunkurin shafe wata al’umma.

Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a birnin Gaza, inda suka kai hari kan unguwannin da ke da yawan jama’a. Katangar da Isra’ila ta kakaba mata da kuma karancin abinci na ci gaba da zurfafa rikicin jin kai.

Yakin da Isra’ila ta kwashe watanni ana yi a Gaza ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama.

Tun daga watan Oktoban 2023, hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza sun kashe a kalla Falasdinawa 64,964 tare da jikkata sama da 165,312, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Yayin da ake fargabar wasu dubbai na  karkashin baraguzan gine gine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted