Ministan man fetur da ma’adanai na gwamnatin tarayyar kasar Somaliya Taha Shari Muhammad ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu aikin da kamfanin kasar Turkiya yake yi na hako man fetur a kasar ya yi nisa, kuma da akwai yiyuwar nan da shekara ta 2026 kasar za ta fara fitar da man Fetur.
Taha Shari ya kuma kara da cewa; Ana gudanar da aikin hako man ne a yankunan “Marig” dake gundumar “Galgadun” da kuma yankin “Harar Tiri” dake gundumar Madga.
Ministan man fetur da kuma ma’adanan na kasar Somaliya ya ce; Idan an gama aiki a wadannan yankunan biyu, za’a nufi garin “ Hobiyo”, don ci gaba da hako wasu rijiyoyin man.
Bugu da kari ministan man fetur na kasar Somaliya ya ce;gwamanti ta na da kwararru wadanda suke yi nazari a kan harkar hakar danyen man fetur, wadanda zasu yi aiki a cikin wani yanayi da ake ciki. Wani kalubalen da minstan ya bijiro da shi, shi ne yadda jiragen kasashen waje suke shiga cikin iyakar ruwan kasar suna aikin neman danyen mai, ba tare da izinin gwamnati ba