Tattaunawar Amurka da Iran ta watse ba tare da cimma yarjejeniya ba

Tawagogin Iran da Amurka sun bar birnin Islamabad na kasar Pakistan gaza cimma wata yarjejeniya.
Tattaunawar Amurka da Iran ta watse ba tare da cimma yarjejeniya ba

Tawagogin Iran da Amurka sun bar birnin Islamabad na kasar Pakistan gaza cimma wata yarjejeniya.

Tawagar Iran karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin kasar ta bar Pakistan da sanyin safiyar ranar Lahadi.
An dai shafe sa’a 21 ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu saidai ba tare da cimma wata matsaya ba.

Tattauanwar ita mafi tsawo da akayi a lokaci guda sannan kuma a matakin koli na manyan jami’ai daga kasar tun bayan juyin juya halin musulinci a Iran a shekarar 1979.

Ita ma tawagar wakilan Amurka, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar, JD Vance, ta koma Amurka bayan gaza cimma yarjejeniya don kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya.

Mista Vance ya bayyana tattaunawar a matsayin mai muhimmanci, amma ya ce bangaren Iran bai amince da abin da ya kira tayin karshe na Amurka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted