Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa

Mahukuntan kasar Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa, ya zuwa yanzu ba a sami wani dalili na musabbabin mutuwar jakadan kasar Nathi Mthethwa A

Mahukuntan kasar Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa, ya zuwa yanzu ba a sami wani dalili na musabbabin mutuwar jakadan kasar Nathi Mthethwa A Afransa ba.

Jami’an tsaron kasar Faransa suna aiki tare da takwarorinsu na kasar Afirka Ta Kudu da su ka isa kasar domin gano musabbabin mutuwar jakadan.

An ga gawar jakadan na kasar na Afirka Ta Kudu a kasar Faransa,Mthethwa a Hotel din Hyatt Regency dake birnin Paris. Alamu sun nuna cewa ya bude kofar dakinsa dake hawa na 22 ya fado kasa, ba tare da wata alama dake nuni da cewa turo shi aka yi baa.

Gabanin faruwar lamarin jakadan ya aike da sako na waya ga maidakinsa da a ciki ya bayyana mata shirinsa na kisan kai.

Kasar Afirka Ta Kudu ta aike da jami’an bincike su biyar zuwa Faransa domin su yi aiki da takwarorinsu na kasar akan binciko hakikanin abinda ya faru.

Mthethwa ya zama jakada ne tun a 2023, bayan da a can baya a kasarsa ya rike mukamai da dama a fagagen al’adu da wasanni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments