Mataimakin ko’odinetan sojojin Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba ta kai matakin da zata samu damar yaƙar Iran ba
Mataimakin ko’odinatan sojojin Iran, Admiral Habibullah Sayyari, ya bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya ba su da ikon yaƙar Iran, kuma bayan Iran ta fara murkushe su, Amurka ta hanzarta shiga cikin yaki, wanda ita ma ta dandana kudarta.”
Da yake jawabi a wani taron jama’a don tunawa da Ranar Yaƙi da Girman Kai ta Duniya, Admiral Sayyari ya ce: “Girman kai yana da halaye uku; na farko shine yana sa ƙasashe su gaza ci gaba, kuma yana mai da hankali sosai kan hakan musamman dangane da Iran.”
Ya ƙara da cewa: “Halayya ta biyu ta girman kai ita ce: Kokarin wawushe duk wani albarkatun duniya. Sannan na uku: Kokarin kare manufofinsa na kashin kansa a matsayi mallakinsa gabaɗaya, ganin Iran tana da albarkatun ƙasa masu yawa, girman kai yana ƙoƙari ganin ya sarrafa su gabadaya. Bayan juyin juya halin 1957, Amurka ta rasa ikonta a kan Iran, yayin da kafin juyin juya halin Musulunci, Iran ta yi aiki a matsayin mai kula da muradun Amurka.”
Mataimakin Ko’odinetan ya ci gaba da cewa: “Juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1957 ya sami damar wargaza ikon Amurka na yaudararta, kuma wannan mummunan rauni ne ga Amurka da girman kai na duniya, godiya ga wannan juyin juya halin na Musulunci.”
Ya nuna cewa: Bayan harin da aka kai wa Iran a shekara ta 1979, “Amurka ta shiga yakin da ƙarfi, tana ƙoƙarin sake mamaye Iran, kuma waɗannan yunƙurin sun haɗa da kisan gillar shahidai 17,000 da kuma yaƙe-yaƙe daban-daban kan ƙasar Iran da nufin sake dawo da iko Amurka.”