Ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinawa ta sanar da cewa adadin shahidai a yankin na Gaza sun kai 50,669, yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai 115,225.
Dangane da rahoton akan shahidan da ake samu a kowace rana kuwa,ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta ce, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 60, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 162.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, da akwai wani adadin na shahidai masu yawa da suke kwance a kasa, ba a iya daukarsu balle a yi musu jana’iza ba, saboda yawansu, da kuma wasu dubbai da suke a karkashin baraguzai na gidajen da makaman HKI su ka rusa da mutane a cikinsu.
A wani labarin daga Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata rumfa ta raba abinci ga Falasdinawa da suke fama a yunwa, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3 a sansanin Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza.
Haka nan kuma sojojin na HKI sun kai hari akan gidajen mutane a cikin garin na Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mututm guda.
Wasu yankunan da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa hare-hare sun hada Qaizan Abu Rashwan dake kudu masu yammacin Khan-Yunus, da Hayyuz-Zaitun da kudu maso gabashin Gaza, sai kuma titin Sakkah a wannan birni.
A gefe daya mutanen Gaza suna ci gaba da yin hijirar da aka tilasta su daga Hayyul-Shuja’iyyah, zuwa yammacin Gaza.