An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52.
Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku.
Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup.
Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma mai tsaron baya na farko tun bayan dan kasar Zaire, Bwanga Tshimen a 1973.
Morocco ce ta lashe yawancin kyautukan da aka raba daga ciki har da ta mace mafi kwazo a 2025 ga Ghizlane Chebbak mai taka leda a Saudiya da mai tsaron ragar Al-Hilal, Yassine Bounou a matakin mafi taka rawar azo a gani a shekarar nan.