Abu Ubaidah: Mun Harbo Sojojin Mamaya 4 Daga Nesa A Beit-Hanun

Mai Magana da yawun dakarun ‘Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa; sun harbo sojojin mamaya 4 ta hanyar wani kwanton bauna da su ka

Mai Magana da yawun dakarun ‘Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa; sun harbo sojojin mamaya 4 ta hanyar wani kwanton bauna da su ka yi musu a Beit-Hanun.

Kakakin dakarun na ” Kassam” ya  kuma ce; Har yanzu suna ci gaba da kwamawa da ‘yan mamaya da kuma yi musu kwanton bauna a wurare mabanbanta.”

Abu Ubadah ya kuma jaddada cewa; ‘yan gwgawarmaya su ne ke zabin lokacin da wurin da za su kai wa abokan gaba hari, kuma jaruntarsu tana bayyana daga garin Beit Hanun zuwa Rafah, da hakan yake a a matsayin abin alfahari ta fuskar soja.

A ranar Alhamis din da ta gabata, ‘yan gwgawarmayar sun harbo sojojin HKI 4 daga cikinsu har da masu manyan mukamai, tare da halaka su da kuma jikkata wasu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments