Kakakin dakarun rundunar “Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa za su saki fursunoni 3 na “Isra’ilawa” a wannan rana ta Asabar.
A jiya Juma’a ne dai kakakin na dakarun rundunar “ Kassam” ya fitar da sanarwar cewa za saki fursunoni uku da suke rike da su da su ne: Shasha Alexander,Sagi Dikel Hen,Yaei Horun
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai mai Magana da yawun dakarun na “Kassam” Abu Ubaidah ta sanar da dakatar da duk wani batu na cigaba das akin fursunonin sai illa masha Allahu. Bayyana wancan matakin dai ya biyo bayan yadda HKI take kin aiki da sharuddan yarjeniyoyin sakin furnsunonin ne da su ka hada da hana mutanen arewacin Gaza komawa gidajensu. Haka nan kuma ci gaba da kai hare-hare a ko’ina a fadin Gaza. Sai kuma hana shigar da kayan aiki domin kwashe baraguzai, magunguna da kuma gidaje na tafi-da gidanka da Falasdinawa za su zauna a ciki.
Sai dai daga ranar Alhamis zuwa jiya Juma’a masu shiga tsakani da su ne kasashen Katar da Masar, sun yi kokarin gusar da matsalar da ta kunno kai daga gefen HKI da hakan ya bayar da damar sake komawa kan batun musayar fursunonin.