Dakarun Ezzeddine al-Qassam, reshen kungiyar gwagwarmayar Hamas masu dauke da makamai, sun sanar a jiya Alhamis shahadar babban kwamandan kungiyar Mohammad “Abu Khaled” Deif tare da wasu manyan kwamandoji da dama, a wani bangare na farmakin guguwar al-Aqsa.
Da yake magana a cikin wani faifan bidiyo da aka fitar ta kafar yada labaran soji ta al-Qassam, mai magana da yawun rundunar Abu Obeida ya ce, sanarwar ta zo ne “bayan kammala dukkan matakan da suka dace da kuma magance dukkan matsalolin tsaro da suke da alaka da yanayin da ake ciki, da kuma bayan gudanar da tantancewar da ta kamata.
“Muna sanar da al’ummarmu, da duk masu goyon bayan ‘yanci da tsayin daka a duniya, shahadar gungun manyan mayaka da kwamandojin rundunar soji ta al-Qassam Brigades,” in ji shi.
Daga cikin shugabannin da suka yi shahada har da Mohammad “Abu Khaled” Deif, kwamandan rundunar Al-Qassam Brigades, tare da Marwan “Abu Baraa” Issa, mataimakin kwamandan rundunar.
“Wannan shi ne abin da ya dace da kwamandan mu Mohammed Deif, Abu Khaled, wanda ya ke fafatwa da makiya sama da shekaru talatin, kuma yanzu ya shiga cikin tarihi na shahidai da suka sadaukar da rayuwarsu a tafarkin Allah da kare gaskiya a cewar Abu Ubaidah.