A Kalla Falasdinawa 35 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A kalla mutane 35 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 62 kuma su ka

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A kalla mutane 35 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 62 kuma su ka jikkata a cikin sa’o’i 24.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kara da cewa; Sojojin Mamaya sun kai wasu hare-hare a gabashin garin Beit-Hanun dake arewacin Gaza.

A cikin hemar ‘yan hijira dake tsakiyar Gaza, Falasdinawa 3 sun yi shahada, bayan da jiragen saman a ‘yan mamaya su ka kai hari.

A kudancin Gaza kuwa sojojin HKI sun tarwatsa wani gini na fararen hula a yankin Misbah dake arewacin birnin Rafah.

Daga ranar 18 ga watan Maris na wannan shekarar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 1864, yayin da wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 4890.

Daga 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu jumillar Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 51,240, sai kuma wani adadin da ya kai na mutane 116, 931, da su ka jikkata.

A gefe daya,kafafen watsa labarun HKI sun bayar da labarin cewa, wani yanayi mai tsanani ya faru a Gaza a yau Litinin,da hakan yake nufin cewa an kai wa sojojinsu hari mai tsanani wanda zai iya zama halaka wasu daga cikinsu.  Haka nan kuma kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa; Uku daga cikin sojojinta sun jikkata saboda fashewar wata nakiya da aka dasa a bakin hanya a Beit-Hanun dake arewacin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments