Cikar Shekaru 43 Da Shahadar Tsohon Shugaba Da Firayi Ministan Iran

Ranar 30 ga watan Agusta na a matsayin ranar yaki da ta’addanci a kasar Iran. Dalilin da ya sa ake kiran wannan rana da wannan

Ranar 30 ga watan Agusta na a matsayin ranar yaki da ta’addanci a kasar Iran.

Dalilin da ya sa ake kiran wannan rana da wannan suna shi ne kisan shugaban kasa  Mohammad Ali Rajaee,  da Dr.Mohammad Javad Bahnar, firaministan kasar na lokacin.

Masu adawa da sabon tsarin Jamhuriyar Musulunci da aka kafa a kasar Iran wadanda gwamnatocin kasashen yammacin duniya ke mara wa baya, suka kashe shugaban kasa da fira minister ta hanyar tayar da bam a ofishin firaministan.

Shugaba Rajaei ya fara ayyukansa  a matsayin malami. A daidai lokacin da yake koyarwa a Jami;a, daga nan kuma ya fara sukar  gwamnatin Shah, ya kuma ci gaba da hakan har zuwa nasarar juyin juya halin Musulunci, a cikin wannan lokacin ya fuskanci matsaloli masu atrin yawa da suka hada da kamu da tsarewa  agidan kaso gami da azabtarwa a hannun jami’an gwamnatin sarki Shah.

Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, Shahid Rajaei ya rike mukaman ministan ilimi, wakili a majalisar dokoki , firaminista da shugaban kasa. A lokacin shugabancinsa, ya zabi Dr. Mohammad Javad Bahnar, malami mai tunani da ilimi wanda ya yi fice wajen yaki da gwamnatin Shah a matsayin firaministansa.

Kasancewar shahidan Rajai da Bahoner mutane ne masu gaskiya da kaskantar da kai, sannan kuma masu himma da tsayin daka wajen cimma manufofin juyin juya halin Musulunci, sun zama abin daga cikin wadanda makiya juyin suka yi ta neman ganin bayansu, wanda kuma daga karshe aka saka musu bam wanda yayi jalinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments