Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin yin aiki tare a cikin himma domin kara fadada alaka tsakanin Iran da Turkmenistan.
Da yake magana yayin ganawarsa da shugaban kasar Turkmenistan Gurbanguly Berdimuhamedow a birnin Tehran a ranar Laraba, Ayatullah Khamenei ya ce yayin da dangantaka tsakanin Iran da Turkmenistan ke bunkasa sosai a cikin ‘yan shekarun nan, akwai sauran damar yin hadin gwiwa.
“Muna fatan cewa a karkashin sabuwar gwamnatin shugaba Pezeshkian, fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da karfi,” in ji jagoran.
Ayatullah Khamenei ya yi karin haske kan ayyukan raya kasa na hadin gwiwa da suka hada da gina babbar hanyar da za ta hada kasashen biyu da kuma shimfida bututun iskar gas na hadin gwiwa, yana mai cewa aiwatar da wadannan ayyuka tare da hadin gwiwar masana Iran, zai kara karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren, Berdimuhamedow ya ce ya gudanar da shawarwari mai kyau da inganci tare da shugaba Masoud Pezeshkian tare da bayyana fatan cewa yarjejeniyar da bangarorin biyu suka rattabawa hannu za ta haifar da sakamako mai kyau.
Har ila yau shugaban na Turkmen ya tuna da marigayi shugaba Ibrahim Raeisi tare da yabawa kokarinsa na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
Berdimuhamedow ya tabbatar da cewa dogon kan iyaka tsakanin Iran da Turkmenistan zai kasance a koyaushe “iyakar zaman lafiya da abokantaka,” ya kuma jaddada shirin gwamnatinsa na fadada alaka a bangarori daban-daban.
Berdimuhamedow ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad da ke birnin Tehran a safiyar yau Laraba domin tattaunawa da jami’an kasar Iran.
Tun da farko ya tattauna da Pezeshkian, kuma bangarorin biyu sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa guda hudu a fannoni daban-daban da suka hada da iskar gas da kwastam.