A yau lahadi ce gwamnatin HKI ta sake sabonta harancin ayyukan watsa labarai na tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon a cikin kasar.
Labarin ya kara da cewa ministan sadarwa Shlomo Karhi ne ya gabatar da bukatar ga majalisar dokokin HKI wacce ta amince da bukatar, sannan Firai ministan kasar ya sanyawa dokar haram Tashar hannu.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin HKI ta bukaci a kwace duk kayakin aikin tashar ta Almayadeen a cikin kasar falasdinu da aka mamaye, sannan a haramta kallon shafinta na yanar gizo a cikin kasar.
Bayan fara yakin tufanul Aksa ma gwamnatin HKI ta haramta tashar na wasu watanni, sannan sojojin HKI sun kashe ma’aikatan tashar guda biyu wadanda suke aikin aiko da rahotanni daga kudancin Lebanon.
Tashar dai tana da yan rahoto da dama a kasar falasdinu da aka mamaye musamman a Gaza.