Dakaru masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun kai hare hare kan sansanin sojojin Amurka mafi girma a kasar Siriya a jiya Asabar.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa jiragen yaki masu kunar bakin wake da dama ne sun fada kan sansanin sojojin Amurka mai suna ‘Ramiilan’ da arewacin kasar Siriya kuma sojojin Amurka da dama sun ji rauni.
Labarin ya kara da cewa, wani babban jami’in sojan Amurka wanda bai son a bayyana sunansa ya tabbatar da aukuwar hare haren ya kuma kara da cewa sojojin Amurka suna bincike don gano yawan asarorin da aka yi.
Sansanin sojojin Amurka na ‘Ramiilan’ dake garin Qamshali a arewa maso gabacin Lardin Hasaka na arewacin kasar Siriya dai, shi ne sansanin sojojin Amurka mafi girma a kasar Siriya.
Amurka tana mamaye da kasar Siriya ne tun shekara ta 2014 da sunan yaki da kungiyar yan ta’adda ta Daesh, wacce ta kirkiro don cimma manufofinta da na HKI a yankin gabas ta tsakiya, amma gwamnatin kasar Siriya tare da taimakon kawayenta sun yaki kungiyar sun kuma sami nasara a kansta a shekara ta 2017.
Sai duk da haka Amurka ta ci gaba da mamayar kasar ta Siriya da sunan yaki da kungiyar Deas wacce babu ita.
Sai kuma bayan fara yakin Tufanul Aksa a cikin watan Octoban shekarar da ta gabata dakaru masu gwagwarmaya da mamayar da sojojin Amurka sukewa kasashen Iraki da Siriya sun sha kai wa wannan sansanin sojojin na Amurka hare hare.