An Kai Munanan Hare-Hare Da Jirage Marasa Matuka A Kan Sansanin Sojin Amurka

A daren jiya an kai wa sojojin Amurka hari da jirage marasa matuƙa a Syria, kamar yadda wani jami’in ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin

A daren jiya an kai wa sojojin Amurka hari da jirage marasa matuƙa a Syria, kamar yadda wani jami’in ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, duk da dai babu wanda ya ji rauni kamar yadda rahotannin farko-farko suka nuna.

“Rahotannin farko ba su nuna cewa an samu wanda ya ji rauni ba, sai dai jami’an lafiya na ci gaba da duba abubuwan da suka faru a wajen. A yanzu haka muna nazari kan ɓarnar da aka yi,” kamar yadda jami’in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana.

Amurka tana da sojoji da dama a Gabas ta Tsakiya, da adadinsu ya kai kimanin 45,000, da sansanoni da dama, da jiragen yaƙi na sama da na ruwa da yawa, abin da ya sa ake nuna damuwa kan yiwuwar ɓarkewar yaƙi a yankin.

A yanzu haka Amurka na da dakaru na musamman da sojoji kimanin 900 a Syria don taimaka wa ƙungiyar ta’addanci ta YPG/PKK, wacce take amfani da sunan SDF.

Amurka na da na ƙananan sansanoni kamar wajen haƙar mai na al-Omar da Al-Shaddadi, mafi yawa a arewa maso gabashin ƙasar, da kuma wani ƙaramin sansanin tsaro na soji, da aka fi sani da sansanin Al-Tanf kusa da iyakar Syria da Iraƙi da Jordan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments