Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya sake nanata cewa, Iran na da hakkin mayar da martani yadda ya kamata kan laifukan da yahudawan sahyoniya suke aikatawa, yana mai jaddada cewa, idan kasashen yammacin duniya suna son rage tabarbarewar tsaro a yankin, to ya kamata su gaggauta dakatar da bayar da goyon baya ga Isra’ila.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ya samu daga takwaransa na Faransa Emmanuel Macron dangane da damuwar da ake da ita kan karuwar tashe-tashen hankula a yankin bayan kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh.
Shugaba Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a yankin da ma duniya baki daya da kuma rage ci gaba da tabarbarewar tsaro da yaki, amma gwamnatin yahudawan sahyoniya bayan ayyukan ta’addanci a kan al’ummar Gaza, da kuma kisan gillar da aka yi wa shahid Haniyyah, wanda ya kasance babban bako na kasar Iran, wunkuri ne na tayar da rigingimu a yankin, wanda Amurka da kasashen yammacin Turai, a maimakon su yi Allah wadai da wannan gwamnati bisa laifukan da ta ke aikatawa, ci gaba da goyon baya suke bata.
Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa, muddin gwamnatin sahyoniyawan tare da goyon bayan siyasa, kudi, kafofin watsa labarai da makamai na Amurka da kasashen yammacin duniya, za su ci gaba da yin kisan kare dangi, da aikata laifuka da kisan gilla cikin zaman lafiya, to kuwa yankin da duniya ba za su samu kwanciyar hankali, da tsaro da, zaman lafiya ba.
Ya kara da cewa idan har Amurka da kasashen yammacin duniya suna son hana barkewar yaki da tabarbarewar tsaro a yankin, da kuma tabbatar da ikirarin da suke yi, to su gaggauta dakatar da sayar da makamai da goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan don dakatar da kisan kiyashi da hare-hare a Gaza da kuma amincewa da tsagaita wuta.