Amurka Ta Kakabawa Iran Sabbin Takunkumai

Amurka ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai. Ma’aikatar kudi ta Amurka ta kakaba sabbin takunkuman ga sassa masu ruwa da tsaki wajen samar da

Amurka ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai.

Ma’aikatar kudi ta Amurka ta kakaba sabbin takunkuman ga sassa masu ruwa da tsaki wajen samar da kayayyakin kera makami masu linzami da jiragai marasa matuka na Iran.

Shafin yanar gizo na ma’aikatar baitul malin Amurka ya sanar yau cewa ofishin mai kula da kadarorin waje (OFAC) ya kakaba takunkumo kan mutane 5 da hukumomi 7 da ke Iran, da China da kuma Hong Kong.

A cikin sanarwar da ma’aikatar baitul malin Amurka ta fitar, an yi ikirarin cewa daidaikun mutane da hukumomin  sun taka rawa wajen “saukake samar da kayayyakin da tallafawa sojojin Iran da kayayakin da suk ke bukata”.

Sanarwar ta Washington ta yi ikirarin cewa mutanen da aka kakabawa takunkuman sun samar da abubuwa daban-daban, ciki har da na’urori masu sauri, wadanda ake amfani dasu wajen kera jiragen sama marar matuki (UAV) na Iran.

Sabbin takunkuman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban kasar Iran, Mas’ud Pezehskian ke kama aiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments